22 Nuwamba 2026 - 09:17
Source: ABNA24
IRGC: Sun Kakkabo Wani Jirgin Mara Matuki Na Leƙen Asirin Amurka A Gabar Tekun Bushehr

Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci sun sanar da lalata wani jirgin mara matuki na leƙen asirin maƙiya a gabar Tekun Bushehr a arewacin Tekun Farisa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci sun sanar da kakkabo wani jirgin mara matuki na leƙen asirin maƙiya a gabar Tekun Bushehr a arewacin Tekun Farisa.

Bisa rahoton cibiyar bayanai ta hukuma ta Sojojin a yammacin ranar Asabar, ma'aikatan Sojojin Sararin Samaniyar Iran, ta hanyar amfani da nagartaccen tsarin tsaron sama, sun yi nasarar gano da lalata jirgin maras matuki na leƙen asiri. Sanarwar ta ce an kakkabo jirgin, wanda ya keta sararin samaniyar Iran, da harbi daidai mai tasiri.

Yayin da suke nanata cewa duk wani keta sararin samaniyar ƙasar ba abin karɓa ba ne kwata-kwata, Sojojin kasar sun kara da cewa ƙoƙarin maƙiya na yin amfani da nau'ikan kayan leƙen asiri da na soji daban-daban zai fuskanci martani kaitsaye kuma mai ƙarfi daga sojojin Iran.

Wannan sanarwar ta zo ne sa'o'i kaɗan bayan da Sojojin IRGC suka ba da rahoton harbo wani jirgin maras matuki na MQ-1 na Amurka a sama da tsibirin Sirik da ke kudancin Iran.

……………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha